Aure akwai wahala: Sai aita damunmu mu yi aure to wa kuke so mu aura?>>Nafisa Abdullahi - arewavid

Breaking

Social Media Widget

BANNER 728X90

Monday, 2 July 2018

Aure akwai wahala: Sai aita damunmu mu yi aure to wa kuke so mu aura?>>Nafisa Abdullahi

Aure akwai wahala: Sai aita damunmu mu yi aure to wa kuke so mu aura?>>Nafisa Abdullahi 
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta fito ta bayyanawa Duniya irin yanda su 'yan mata ke shan wahala wajan samun masoya a wannan zamani, Nafisa tace duk sai abi ai ta damunsu wai sunki aure, to wa ake so su aura?.


Ta kara da cewa samun masoyi na gaskiya a wannan zamani akwai wahala, kuma ita gaskiya kawai dan tna so tayi aure ba zata auri wanda be mata ba. Tace, idan kana soyayya da me aure, akwai sa ciwon kai, matarshi tabi ta dame ka, bata so ka shiga gidan haka shima duk ya bi ya dame ka, to wai yaya zamuyi ne?, haka ma samarin yanzu duk suna da wanda suke so, suna da 'yan mata, idan ma ana soyayya dake anayi ne a boye ba'aso ta bayyana.


Ta kara da cewa, wani abin damuwa ma samarin yan zun yawanci basu nutsu suka san me ke musu ciwo ba, basu zama cikakkun mutane ba, sai shaye-shaye da kwambo ana daukar hotuna ana sakawa a yanar gizo.


Wani ya cewa Nafisar idan bera da sata daddawa ma da wari, 'yan matan na yanzune buri ya musu yawa, Nafisar ta bashi amsar cewa, matsalar ba a buri take ba, dan akwai me dogon buri akwai me matsakaici akawai kuma wadda duk wanda ta samu bata da matsala, tace kai akwai wadda ma ita bata san me take so ba, amma a cewarta, buri ba laifi bane dan mace tana dashi.
A karshe dai Nafisar tace, sudai gasu ga Allah, suna fatan yayi musu zabi mafi Alheri.

No comments:

Post a Comment