Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg yana fuskantar matsin lamba kan bukatar ya bayyana domin a bincike shi a kan abun da shafin nasa ke yi.
Ana zargin kamfaninsa da kin shaida wa masu amfani da shi cewar ana tattara bayanan da suka sanya a shafukansu da kuma ajiye su a wani kamfanin sadarwa na Cambridge, wanda da aka sani wajen taimakawa Donald Trump lashe zaben shugaban kasa a 2016.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne Facebook ya ce ya toshe kamfanin Cambridge Analytica daga shafin, yayin da yake bincike kan korafin cewa kamfanin mai cibiya a Landan bai goge bayanan da ake zargi ya samu ta hanyar karya ka'idojin Facebook ba kamar yadda ya yi alkawari.
Dukkan kamfanonin biyu dai Cambridge Analytica da Facebook sun yi watsi da batun cewa sun aikata ba daidai ba.
Tuni hannayen jarin Facebook suka fara yin kasa sakamakon matsin lambar da ya ke fuskanta.
Duk da alwashin da ya sha a 2018 cewa zai gyara kamfanin nasa, Mark Zuckerberg ya yi kokarin kaucewa sukar da yake sha daga dumbin mutane - a maimakon haka sai yake ta aike lauyoyi zuwa kwamitoci domin sauraron korafe-korafe.
An wallafa kalaman Zuckerberg na baya-bayan nan a kan wasu ce-ce-ku-cen da ke faruwa kan Facebook a wani kebabben shafin intanet, sannan aka wallafa a shafinsa na Facebook din.
Yayin da ake kara nuna damuwa kan yadda bayanan da Facebook ke tatattarawa za su kara iza wutar farfagandar siyasa, wasu manyan masu fada a ji a karshen wannan makon sun ce lokaci ya yi da Mista Zuckerberg zai kara kaimi don fitowa fili ya kare kansa kan wannan batu.
Wasu ma sun yi kira da a yi bincike kan ko kamfanin Mista Zuckerberg ya karya wasu dokoki na tattara bayanai, da kuma dokokin rashin samun izinin masu amfani da shafin don tattara bayanan da suka shafe su.
No comments:
Post a Comment