Wata budurwa mai kimanin shekara 19 mai suna Hafsat Aminu ta hallaka kanta bayan ta sha kanarzir ta kuma yi wanka da shi kana ta banka wa kanta wuta sakamakon yunkurin raba ta da saurayinta wanda kuma dan uwa ne gare ta.
Hafsat Aminu ta rasu ne duk da kokarin da likitoci suka yi wajen ceton rayuwarta a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu da kuma Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano inda ta cika kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Lamarin ya faru ne a makon jiya a Titin Salihi da ke Unguwar kofar Fada da ke cikin garin Birnin Kudu.
Majiyarmu ta mahaifiyar Hafsa mai suna Abu ta rabu da mahaifin
Hafsa kimanin shekara 17 da suka gabata
Majiyarmu ta ce bayan Hafsat ta kona kanta ne sai uban goyonta mai suna Malam Abubakar Ahmed Gumel da mahaifiyar Hafsa suka dauke ta zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu, inda yake aiki domin ceton rayuwarta, majiyar ta ce da lamarin ya gagara sai aka garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Mahaifin Hafsat, Malam Aminu Yakubu wanda malami ne a Makarantar Sakandaren Arabiyya da ke Birnin Kudu ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar ’yarsa Hafsa kuma ya ce rabonsa da ita shekara 17, tana wajen mahaifiyarta saboda aurensu ya kare.
Ya ce ya samu labarin rasuwarta ne yana wanka aka yi sallama ya fito aka gaya masa cewa Hafsa ta kone bayan ta sha kananzir ta sanya wa kanta wuta.
Ya ce har zuwa lokacin da yake magana da Aminiya bai san abin da ya yi sanadin mutuwarta ba amma dai an fada masa cewa ita ce ta sa wa kanta wuta ta kone.
Malam Aminu ya ce “Yaron da ake cewa yana soyayya da ita dan uwana ne ba ya da wata matsala kuma babu batun maganar auren dole, kamar yadda ake bazawa wai za a yi mata shi ne ya sa ta kone kanta. In takaita maka labarai mahaifin yaron nan shi ne ma ya sayi goron daurin aurena da mahaifiyar Hafsa saboda haka batun a ce wai auren dole za a yi mata ta hallaka kanta ba gaskiya ba ne.”
Ya ce bana ta kammala sakandare, kuma yanzu haka sunanta yana cikin jerin daliban da aka dauka domin yin karatun fannin lafiya a Makarantar Ungozoma ta Birnin Kudu, sai ya ce kwananta ne ya kare kuma ba ya da wani abu da zai fada illa Allah Ya jikanta Ya yi mata rahama.
Saurayin Hafsa mai suna Haruna Ibrahim wadda tela ne a Titin Salihi ya ce tsawon soyayyarsu da Hafsa bai wuce wata 8 ba, amma sun yi matukar shakuwa da juna kuma ba ya jin nan gaba zai iya samun wata budurwa da za ta nuna masa irin son da Hafsa take masa.
Ya ce batun karatu da ake yi a kansa gaskiya ne ya kammala karatunsa na NCE a Gumel, kuma ya ce batun Hafsa ta hallaka kanta ta hanyar sha kananzir kuma ta yi wanka da shi ta kone kanta gaskiya ne.
Amma ya ce cewar da ake yi saboda shi ne ta hallaka kanta ba gaskiya ba ce, ya ce yana da labarin Hafsa tana fama da aljanu domin a lokacin da ta aikata hakan ma da ta dawo cikin hankalinta mamakin yadda abin ya faru ta rika yi.
Haruna Ibrahim ya ce a iya fahimtarsa da ita tana da aljanu kuma su ne suka sa ta aikata hakan ba wai soyayyar da take masa ba ce. Ya ce ai a cikin soyayyarsu babu batun wata magana ta kiyayya ko batun auren dole saboda ba a ma fara maganar aure ba ballanta batun kiyayya ya taso.
Ya ce rasuwar Hafsa ta firgita shi matuka lura da labarin ta rasu ne sakamakon konewar da ta yi. Kuma ya musanta labarin cewa ta aika masa da sakon tes kafin ta rasu, inda ya ce babu wani sako da ta rubuta masa.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci Cibiyar Kiwon Lafiya da ke Birnin Kudu don jin ta bakin mahaifiyar Hafsat, uban goyon Hafsat kuma mijin mahaifiyarta Malam Abubakar Ahmed Gumel ya ki amincewa a yi magana da iyalinsa. Ya rika fada yana cewa “Ni kulle nake yi ba zan bari a yi magana da iyalina ba ai ni ba arne ba ne Musulmi ne. Ba zai yiwu in bar wani ya yi magana da matata ba. Ai mutuwa tana kan kowa kowa zai mutu kuma kowa da yadda Allah Ya rubuta zai koma gare Shi babu dalilin da zai sa in yi magana da ku kuma ba zan bar matata ta yi magana da ku ba.”
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa Abdul Jinjiri ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba.
No comments:
Post a Comment