Na taba yin aure amma yanzu Banda aure Sai dai Niyya - Inji Aina'u Ade Laila - arewavid

Breaking

Social Media Widget

BANNER 728X90

Monday, 19 March 2018

Na taba yin aure amma yanzu Banda aure Sai dai Niyya - Inji Aina'u Ade Laila

Sau da yawa wasu kan yi mamakin yadda wasu yaruka daban ke shiga cikin duniyar fina-finan Hausa su yi ta fantamawa suna rawar gaban hantsi. 

Wannan ya sa a wannan karon Taurarin Nishadi ya tattauna da wata Bayarabiya da ta ga jiya kuma take ganin yau a duniyar fina-finan domin warware wa mutanen da ke wancan mamakin yadda lamarin yake.

Wakiliyarmu, JUMMAI IBRAHIM ta tattauna da jarumar. A sha karatu lafiya: Ya cikakken sunan jarumar?

Sunana Ainau Ade, ni Bayarabiya ce, amma a nan Kano aka haife ni.

Ya cikakken sunan jarumar?

Sunana Ainau Ade, ni Bayarabiya ce, amma a nan Kano aka haife ni.
ji cikaken tarihin ki da abun da ya jawo ra’ayinki kika shiga harkar fim din Hausa, da wane fim kika fara kuma a wace shekara kika fara?

Ni ai tsohuwar ‘yar fim ce, bai ma kamata ki tambaye ni ra’ayina na shiga fim ba.

Wanan tambayar sai dai ki mika ta ga sabbin zuwa. Ta yaya kike hada harkokinki da kula da iyali

A yanzu dai ba ni da aure gaskiya amma lokacin da aka daina ganina a fim ina gidan mijina ne lokacin, don na yi aure ina da yara guda biyu, kuma ai harkar fim ba zai hana ni ‘business’ dina ba, ina da shago kuma ina ba da kaya ga masu siyan daya-daya ko sari.

Wane fim ne cikin finafinanki ya fi burge ki?

Ni fa Yanzu daga na ji an ce ‘action’ sai kawai na ga na fara zaro bayyanai, ban sani ba, ko don abin ya riga ya zame min jiki ne, oho, kuma gaskiya ba ni da wani fim din da ya ban wahala, kuma duk fim din da ba zai burge ni ba ba zan ma karbe shi ba, don haka duk fim din da na yi suna burge ni. 

Bayan haka za ki ga an ciri wani ‘scene’ ana yawo da shi a waya tsabar ya burge mutane.

No comments:

Post a Comment