Wani Saurayi Ya Auri Mata biyu a Rana Daya A Kasar Somalia. - arewavid

Breaking

Social Media Widget

BANNER 728X90

Monday 2 July 2018

Wani Saurayi Ya Auri Mata biyu a Rana Daya A Kasar Somalia.


Wani saurayi dan kasar Somaliya da ya auri mata biyu a rana daya, ya ce ya yi hakan ne don ya karfafa wa maza gwiwa kamar yadda ya shaida wa BBC.


Saurari mai suna Bashir Mohammed ya ce ya fara soyayya da 'yan matan biyu ne kimanin watanni takwas da suka wuce kafin su amince da bukatarsa ta aurensu.
"Na rika kawo 'yan matan gidana domin su saba da ni. Kuma a duk lokacin da muke tare da su ina fada musu yadda nake kaunarsu. Kuma dukanninsu sun gamsu da hakan," in ji sabon angon.


"Dabarar auren mata biyu tashi guda shi ne ba za su rika nuna tsananin kishi ba daga bisani, saboda kowace za ta fahimci cewa ba ita kadai ba ce," a cewarsa.


Matashin ya ce ya auri mata biyu ne tashi guda saboda yana "son yara da yawa".


Gabilin al'ummar kasar Somaliya Musulmi ne wadanda addininsu ya amince musu su auri mace fiye da daya.


Sai dai ba a saba ganin saurayi ya auri mata biyu ba a rana guda, in ji wakilin BBC Mohamed Mohamed.


Ba wannan ne karon farko da hakan ya faru a kasar ba domin ya taba faruwa a shekarun baya, abin da ya sa wadansu suke ganin watakila a ci gaba da raya al'adar a kasar.


Ango Bashir ya aure matan biyu ne masu suna Iqra da Nima a ranar Juma'a a kauyen Sinai wanda ke karkashin yankin da ya balle daga Somaliya wato Somaliland.

No comments:

Post a Comment