ADAM ZANGO YAYI FIM DA TSOHUWAR MATARSA - arewavid

Breaking

Social Media Widget

BANNER 728X90

Monday 19 March 2018

ADAM ZANGO YAYI FIM DA TSOHUWAR MATARSA


Tsohuwar jaruma Maryam Abdullahi wadda akafi sani da Maryam Ab Yola tsohuwar matar Jarumi Adam A Zango ta uku wadda suka rabu a shekarun da suka wuce.  Jaruman dai kafin aurensu sunyi finafinai Irinsu NASS da ALKAWARI tare.

Zango da Maryam sunyi aure a 2013 bayan gama daukar film din NASS, An daura auren ne a Lugbe wata Unguwa a garin Abuja. Sun rabu bayan ta haifa masa yaro daya.
Wani abin mamaki shine Maryam yanzu ta dawo film ta hanyar tsohon mijinta inda ya sakata acikin wani shirin film Dinshi mai suna RAMAKON GAYYA wanda Bello Muhammad Bello yake bada Umarni.

Yanzu haka dai angama daukar kashin farko na film din,  zuwa nan gaba za'a cigaba.

No comments:

Post a Comment